عَنْ أَبِي مُـحَمَّدٍ الحَسَنِ بْنِ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ - سِبْطِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَرَيْحَانَتِهِ-، قَالَ: حَفِظْتُ مِنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«دَعْ مَا يَرِيبُك إلَى مَا لَا يَرِيبُكَ».
[صحيح] - [رواه الترمذي والنسائي] - [الأربعون النووية: 11]
المزيــد ...
Daga Abu Muhammad al-Hasan ibnu Ali Ibnu Abi Ɗalib - jikan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma abin shinshinarsa -, ya ce: Na haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -:
«Kabar abinda kake kokwantansa, zuwa ga abinda baka kokwantansa».
-
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da barin abin da kake kokwanto akansa na maganganu da ayyuka cewa shin an hana kuwa ko a'a, shin haramun ne ko halal ne, zuwa ga abin da baka kokwanto a cikinsa daga abin da ka tabbatar da kyawunsa da kuma halaccinsa.