Karkasawa:
+ -

عَنْ أَبِي يَعْلَى شَدَّادِ بْنِ أَوْسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ اللهَ كَتَبَ الْإِحْسَانَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ، فَإِذَا قَتَلْتُمْ فَأَحْسِنُوا القِتْلَةَ، وَإِذَا ذَبَحْتُمْ فَأَحْسِنُوا الذِّبْحَةَ، وَلْيُحِدَّ أَحَدُكُمْ شَفْرَتَهُ، وَلْيُرِحْ ذَبِيحَتَهُ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [الأربعون النووية: 17]
المزيــد ...

Daga Abu Ya'ala Shaddadu ibnu Aws - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Lallai Allah Ya wajabta kyautatawa akan kowanne abu, idan zaku yi kisa to ku kyautata kisan, kuma idan zaku yi yanka to ku kyautata yankan, kuma ɗayanku ya wasa wuƙar tasa, don ya hutar da abin yankansa»

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [الأربعون النووية - 17]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki Ya wajabta mana kyuatayi a kowane abu, kyuatatawa; ita ce jin tsoron Allah a halin dawwama a bautarsa, da kuma yin alheri da kame cuta ga ababen halitta, yana daga wannan kyautatawar a kisa da yanka.
Kyautatawa a kisa a lokacin yin ƙisasi: Shi ne ya zaɓi mafi sauƙin hanyoyi, kuma mafi saurinsu a fitar rai ga wanda za'a kashe.
Kyautatawa a yanka: Shi ne ya tausasawa dabba ta hanyar wasa abin da za ayi yankan da shi, kuma kada a wasa a gaban abin da za a yanka ɗin, alhali tana kallon abin da za a yi yankan da shi, kuma kada a yanka alhali akwai wasu dabbobin da suke kallon wadda za a yanka.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - da tausasawarsa ga halitta.
  2. Kyautata kisa da yanka: shi ne ya kasance ta fuskar da shari'a ta halatta.
  3. Cikar shari'a da tattaruwarta a kan kowane alheri, yana daga cikin hakan jin ƙan dabbobi da tausasawa garesu.
  4. Hani daga musla ga mutum bayan kasheshi
  5. Haramta dukkanin abin da a cikinsa akwai azabtarwa ga dabbobi.
Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci الأمهرية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الدرية الصربية الطاجيكية Kinyarwanda المجرية التشيكية الموري الولوف Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية الجورجية المقدونية الخميرية
Manufofin Fassarorin
kashe kashe
Kari