عَنْ جَابِرٍ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ مِنْ أَحَبِّكُمْ إِلَيَّ وَأَقْرَبِكُمْ مِنِّي مَجْلِسًا يَوْمَ القِيَامَةِ أَحَاسِنَكُمْ أَخْلاَقًا، وَإِنَّ أَبْغَضَكُمْ إِلَيَّ وَأَبْعَدَكُمْ مِنِّي مَجْلِسًا يَوْمَ القِيَامَةِ الثَّرْثَارُونَ وَالمُتَشَدِّقُونَ وَالمُتَفَيْهِقُونَ»، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، قَدْ عَلِمْنَا الثَّرْثَارُونَ وَالمُتَشَدِّقُونَ فَمَا الْمُتَفَيْهِقُونَ؟ قَالَ: «الْمُتَكَبِّرُونَ».
[صحيح] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 2018]
المزيــد ...
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Lallai wanda ya fiku soyuwa a gare ni kuma mafi kusancinku mazauni a ranar AlKiyama (su ne) mafi kyawunku halayya, kuma mafi ƙinku a gare ni, kuma mafi nisantarku dani a mazauni a ranar AlKiyama masu yawan surutu da masu tsanantawa, da masu jiji da kai», suka ce ya Manzon Allah, haƙiƙa mun san masu yawan surutu da masu tsanantawa to su waye masu jiji da kai ya ce: «Masu girman kai».
[Ingantacce ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi] - [سنن الترمذي - 2018]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya bayyana cewa yana daga mafi soyuwarku gare shi a duniya, kuma mafi kusancinku mazauni da shi a ranar Alkiyama (su ne) mafi kyawunku a ɗabi'u, kuma cikin mafi ƙiyayyarku gare shi a duniya, kuma mafi nisantarku mazauni daga gare shi a ranar Alkiyama masu munanan ɗabi'u a cikinku; (masu yawan surutu) sune masu yawaita magana dan ɗorawa kai da kuma fita daga gaskiya, (masu tsanantawa kuwa) sune masu yalwatawa a cikin zance dan ɗorawa kai fasaha da girmama maganarsu ba tare da kiyayewa ba, (da masu girman kai). suka ce: Ya Manzon Allah, haƙiƙa mun san masu yawan surutu da masu tsanatwa, to su waye masu jiji da kai? Ya ce: masu girman kai masu yi wa mutane izgili wadanda suke yawaita magana kuma suke bude bakunansu da shi.