عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما قال:
لَمْ يَكُنِ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَاحِشًا وَلَا مُتَفَحِّشًا، وَكَانَ يَقُولُ: «إِنَّ مِنْ خِيَارِكُمْ أَحْسَنَكُمْ أَخْلَاقًا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3559]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Bn Amr -Allah Ya yarda da su- ya ce:
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taɓa kasance wa mai alfasha ba, ko mai ƙoƙarin alfasha ba, ya kasance yana cewa: Lalle masu kyawawan dabi’unku suna cikin zaɓaɓɓunku.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3559]
Mummunar magana ko mummunan aiki ba su kasance cikin dabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba, bai nufe shi ba, kuma bai ganganta yinsa ba, to, shi fa [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ma’abocin ɗabi’u ne masu girma.
Kuma [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana cewa: Lalle mafi falalarku a wurin Allah mafi kyawunku kyawawan ɗabi’u, ta hanyar bayar da abu mai kyau, da sakin fuska, da kamewa daga cutarwa, da juriya, da hulɗa da mutane da abu mai kyau.