Karkasawa:
+ -


____

[] - []
المزيــد ...

Daga Abu Mas'ud Uƙbah ibnu Amr al-Ansari al-Badri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Yana daga abin da mutane suka riska daga zancen Annabci na farko: Idan ba ka da kunya, to ka aikata abin da kake so".

[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [الأربعون النووية - 20]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa daga abinda ya zo a cikinsa wasicci game da Annabawa magabata, kuma mutane suka jujjuya shi tsakaninsu kuma suka gaje shi daga garesu ƙarni bayan ƙarni, har sai da yakai zuwa farkon wannan al'ummar, ka duba zuwa abinda kake son ka aikata shi, idan ya kasance abinda ba'a jin kunyarsa ne to ka aikata shi, idan ya kasance daga abinda ake jin kunyarsa ne to ka bar shi; domin abinda yake hana munanan ayyuka shi ne kunya, wanda ba shi da kunya, to sai ya kutsa a cikin kowace alfasha da abin ƙi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kunya asalin manyan ɗabi'u ce.
  2. Kunya, siffa ce daga siffofin Annabawa - aminci ya tabbata agare su -, kuma ita tana daga abinda aka cirato daga garesu.
  3. Kunya ita ce wacce take sanya mutum musulmi ya aikata abinda zai sa shi kyau kuma ya ƙaway a shi, kuma ya bar abinda zai munana shi ya aibata shi.
  4. Nawawi ya ce: Umarni a cikinsa dan halacci ne, wato: Idan ka yi nufin aikata wani aiki idan ya kasance daga abinda baka jin kunyar Allah da ManzonSa ne idan ka aikata shi to ka aikata shi, inba haka ba to a'a (kada ka aikata) akan haka Musulunci yake, fuskantar hakan cewa abinda aka yi umarni da shi na wajibi ko na mandubi ana jin kunyar barinsa, abinda kuma aka hana na haram da makaruhi to ana jin kunyar aikata shi, amma abin da aka halatta aikata shi da barinsa to jin kunya a aikata shi ya halatta, haka nan a barinsa, sai hadisin ya ƙunshi hukunce-hukunce guda biyar. Akace:
Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy الفولانية Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch اليونانية الأكانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية الخميرية الماراثية
Manufofin Fassarorin
kashe kashe
Kari