عن عائشة رضي الله عنها قالت: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«إنَّ المُؤْمِنَ ليُدرِكُ بِحُسْنِ خُلُقِهِ دَرَجَةَ الصَّائِمِ القَائِمِ».
[صحيح بشواهده] - [رواه أبو داود وأحمد] - [سنن أبي داود: 4798]
المزيــد ...
Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
Lalle mumini yana riska da kyawawan dabi’unsa matsayin mai azumi da mai tsayuwar dare.
[Ingantacce ne a baki dayan Riwayoyin sa] - - [سنن أبي داود - 4798]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana kyawawan ɗabi’u suna kai mai yin su matsayin mai azumi kullun da rana kuma mai Nafila da daddare, matattarar kyawawan ɗabi’u ita ce: bayar da kyakkyawan abu, da kyakkyawar magana, da sakin fuska da rashin cutar da mutane da jure cutarwarsu.