عن أنس بن مالك رضي الله عنه مرفوعاً: «إن الله ليرضى عن العبد أن يأكل الأكلة، فيحمده عليها، أو يشرب الشَّربة، فيحمده عليها».
[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...
An rawaito daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Lallai Allah yana yarda da Bawa kan cewa yaci abinci, sannan ya gode kan hakan, ko yasha abun sha, sai ya godewa Allah kan hakan"
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi]
yana daga cikin abubuwan da suke janyo Yardar Allah Madaukaki gode masa kan abinci ko Sha saboda Allah Madaukai shi kadai ne mai bada falala da wannan Arzikin