عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ:
سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «قَالَ اللَّهُ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: يَا ابْنَ آدَمَ إِنَّكَ مَا دَعَوْتَنِي وَرَجَوْتَنِي غَفَرْتُ لَكَ عَلَى مَا كَانَ فِيكَ وَلاَ أُبَالِي، يَا ابْنَ آدَمَ لَوْ بَلَغَتْ ذُنُوبُكَ عَنَانَ السَّمَاءِ ثُمَّ اسْتَغْفَرْتَنِي غَفَرْتُ لَكَ، وَلاَ أُبَالِي، يَا ابْنَ آدَمَ إِنَّكَ لَوْ أَتَيْتَنِي بِقُرَابِ الأَرْضِ خَطَايَا ثُمَّ لَقِيتَنِي لاَ تُشْرِكُ بِي شَيْئًا لأَتَيْتُكَ بِقُرَابِهَا مَغْفِرَةً».
[حسن] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 3540]
المزيــد ...
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - ya ce:Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kwaɗayi gareni zan gafarta maka abinda ya kasance gareka babu ruwaNa, Ya kai ɗan Adam da zunubanka sun kai ƙololuwar sama sannan ka nemi gafarata zan gafarta maka, babu ruwaNa, Ya kai ɗan Adam lallai cewa kai da ka zo min da kurakurai cikin ƙasa sannan ka gamu dani ba yi min tarayya da wani abu ba, da na zo maka da gafara cikinta".
[Hasan ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi] - [سنن الترمذي - 3540]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari cewa Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya faɗa a cikin hadisi Kudisi:
Ya kai ɗan Adam muddin dai kana roƙoNa kana kwaɗayin rahamata, ba ka yanke ƙauna ba; zan suturta zunubanka zan shafesu batare da kulawa ba a cikinsu; koda wannan zunubin da sabon sun kasance daga manyan zunubai ne. Ya kai ɗan Adam ! Da zunubanka sun yawaita yawan da zasu cika abinda ke tsakanin sama da ƙasa ta inda suka kai sasanninta kuma suka game gefanta, sannan ka nemi gafarata; zan shafe zan gafarta maka dukkaninsu ba tare da kulawa da yawansu ba.
Ya kai ɗan Adam: Lallai kai da zaka zo min bayan mutuwa da zunubai da sabo cikin ƙasa, kuma ka zama mai tauhidi baka taranya wani abu daNi ba; dana fuskanci waɗannan zunuban da sabon da gafara cikin ƙasa; domin cewa Ni Mai yalwar gafar ne, kuma ina gafarta dukkan zunubai in banda shirka.