+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ:
قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ اللَّهَ قَالَ: مَنْ عَادَى لِي وَلِيًّا فَقَدْ آذَنْتُهُ بِالحَرْبِ، وَمَا تَقَرَّبَ إِلَيَّ عَبْدِي بِشَيْءٍ أَحَبَّ إِلَيَّ مِمَّا افْتَرَضْتُ عَلَيْهِ، وَمَا يَزَالُ عَبْدِي يَتَقَرَّبُ إِلَيَّ بِالنَّوَافِلِ حَتَّى أُحِبَّهُ، فَإِذَا أَحْبَبْتُهُ: كُنْتُ سَمْعَهُ الَّذِي يَسْمَعُ بِهِ، وَبَصَرَهُ الَّذِي يُبْصِرُ بِهِ، وَيَدَهُ الَّتِي يَبْطِشُ بِهَا، وَرِجْلَهُ الَّتِي يَمْشِي بِهَا، وَإِنْ سَأَلَنِي لَأُعْطِيَنَّهُ، وَلَئِنِ اسْتَعَاذَنِي لَأُعِيذَنَّهُ، وَمَا تَرَدَّدْتُ عَنْ شَيْءٍ أَنَا فَاعِلُهُ تَرَدُّدِي عَنْ نَفْسِ المُؤْمِنِ، يَكْرَهُ المَوْتَ وَأَنَا أَكْرَهُ مَسَاءَتَهُ».

[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 6502]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: ""Lallai Allah Ya ce: Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da shi, kuma bawaNa bai taba kusanta zuwa gare Ni ba da wani abu kamar abinda na farlanta masa ba, bawa Na ba zai gushe ba yana kusanta gareNi da nafilfili har sai Na soshi, idan Naso shi zan zama jinsa da yake ji da shi, da ganinsa da yake gani da shi, da hannunsa da yake dauka da shi, da kafarsa da yake tafiya da ita, kuma da zai rokeni sai na ba shi, kuma da zai nemi tsari da Ni sai Na tsare shi, kuma ban taba kai komo a kan yin wani abu kamar karbar ran mumini ba, yana kin mutuwa Ni kuma iNa ki masa wahalarsa"

[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6502]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin a cikin Hadisi Kudsi cewa Allah - Mai girma da daukaka - Ya ce: Wanda ya cutar da wani masoyi daga masoyana ya fusatar da shi ya ki shi to hakika Na sanar da shi na shelanta masa kiyayya.
Waliyyi shi ne: Mumini mai tsoron Allah, kuma gwargwadan abinda ke ga bawa na imani da tsoron Allah rabonsa na walicci yake kasancewa. Musulmi bai nemi kusanci ga Ubangijinsa ba da wani abu daga abinda Ya fi soyuwa gare Shi kamar wanda ya wajabta masa na aikata biyayya da barin abubuwan da aka haramta, kuma musulmi ba zai gushe ba yana kara kusanci ga Ubangijinsa da nafilfili tare da farillai ba; Har sai ya samu soyayyar Allah. Idan Allah Ya so shi, to Allah Zai zama Mai daidaita shi a wadannan gabobin guda hudu:
Zai daidaita shi a jinsa, ba zai ji komai ba sai abinda Allah Ya yarda da shi.
Kuma Zai daidaita shi a ganinsa, ba zai kalli komai ba sai abinda Allah Yake son kallo zuwa gare shi kuma Ya yarda da shi.
Kuma Zai daidaita shi a hannunsa, ba zai aikata komai da hannunsa ba sai abinda zai yardar da Allah.
Kuma Zai daidaita shi a kafarsa, ba zai yi tafiya ba sai inda zai yardar da Allah, kuma ba zai yi wani kokari ba sai abinda acikinsa akwai alheri.
A tare da hakan idan ya roki Allah wani abu to lallai Allah zai ba shi abinda ya roka, sai ya zama wanda ake amsawa addu'a, idan ya nemi tsarin Allah ya fake gareShi dan neman tsari, to cewa Allah Zai tsare shi Zai kare shi daga abinda yake jin tsoro.
Sannan Allah - Madaukakin sarki - Ya ce: Ban yi wani kai kawo ba game da wani abu da Ni zan aikata shi ba kamar kaikawo Na a karbar ran mumini dan tausayinsa; Domin shi yana kin mutuwa, dan abinda ke cikinta na radadi, Allah kuma Yana kin abinda zaisa mumini jin radadi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wannan Hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudusi ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu kususiyyar Alƙur'ani a cikinsa, waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, na bauta da karanta shi, da alwala saboda shi da tahaddi (fito na fito) da gajiyarwa (I’ijazi) da wanin hakan.
  2. Hani daga cutar da waliyan Allah da kwaɗaitarwa a son su, da iƙirari da falalarsu.
  3. Umarnin gaba da maƙiya Allah da haramta jiɓintarsu.
  4. Wanda ya yi da'awar walittaka ba tare da bin shari'ar Allah ba to shi maƙaryaci ne a da'awarsa.
  5. Ana samun walittaka a wurin Allah ne ta hanyar aikata wajibai da barin abubuwan da aka haramta.
  6. Daga sabubban son Allah ga bawa da amsa Addu’ar sa aikata nafilfili bayan tsayuwa da wajibai da barin abubuwan da aka haramta.
  7. Nuni akan ɗaukakar waliyyai da ɗaukakar matsayinsu.
Kari