عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما أن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«الرَّاحِمُونَ يَرْحَمُهمُ الرَّحمنُ، ارحَمُوا أهلَ الأرضِ يَرْحْمْكُم مَن في السّماء».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي وأحمد] - [سنن أبي داود: 4941]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Masu jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman yana jin ƙansu, ku ji ƙan mutanen ƙasa wanda ke sama zai ji ƙanku".
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 4941]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa waɗanda suke jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman Yana jin ƙan su da rahamarSa wacce ta yalwaci kowanne abu; don sakayyar da ta dace.
Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi umarni da jin ƙan waɗanda ke ƙasa mutum ne, ko dabba, ko tsuntsu, ko waninsa na nau'ikan halitta sakamakon hakan (shi ne) Allah Zai ji kanku daga saman sammanSa.