+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«الْمُؤْمِنُ الْقَوِيُّ، خَيْرٌ وَأَحَبُّ إِلَى اللهِ مِنَ الْمُؤْمِنِ الضَّعِيفِ، وَفِي كُلٍّ خَيْرٌ، احْرِصْ عَلَى مَا يَنْفَعُكَ، وَاسْتَعِنْ بِاللهِ وَلَا تَعْجَزْ، وَإِنْ أَصَابَكَ شَيْءٌ، فَلَا تَقُلْ لَوْ أَنِّي فَعَلْتُ كَانَ كَذَا وَكَذَا، وَلَكِنْ قُلْ قَدَرُ اللهِ وَمَا شَاءَ فَعَلَ، فَإِنَّ (لَوْ) تَفْتَحُ عَمَلَ الشَّيْطَانِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2664]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne, ka yi kwadayin yin abinda zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kada ka gaza, idan wani abu ya sameka kada ka ce: Dana aikata da kaza da kaza ya kasance, sai dai ka ce : Kaddarar Allah abinda Ya so zai aikata, domin cewa (da a ce) tana bude aikin Shaidan".

Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa mumini gaba dayansa alheri ne , sai dai mumini kakkarfa a imaninsa da kudirin niyyarsa da dukiyarsa da wasunsu daga fuskokin karfi shi ne mafi alheri kuma mafi soyuwa ga Allah - Mai girma da daukaka - daga mumini rarrauna. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa mumini wasicci da yin riko da sabubba a cikin abinda zai anfane shi na al'amuran duniya da lahira, tare da dogaro ga Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka -, da neman taimakonSa, da dogaro gareShi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga gajiyawa da kasala da nauyayawa game da aikata abinda zai yi amfani a duniya da lahira. Idan mumini ya yi kokari a aiki, ya yi riko da sabubba, yana mai neman taimakon Allah, da neman alheri daga Allah, to babu komai akansa sai ya fawwala al'amarinsa gaba dayansa ga Allah, kuma ya sani cewa zabin Allah - Mai girma da daukaka - shi ne alheri. Idan wata musiba ta same shi bayan hakan , to kada ya ce: "Da a ce, ni na aikata da kaza da kaza ya kasance"; "Domin cewa (Da a ce) tana bude aikin Shaidan" A bujirewa kaddara, da dana sani akan abinda ya wuce, sai dai ya ce yana mai mika wuya kuma yana mai yarda: "Kaddarar Allah, abinda Ya so zai aikata", abinda ya afku , kawai shi da hukuncin abinda Allah ya so ne, domin cewa Shi mai aikata abinda Ya yi nufi ne, kuma babu mai juyar da hukuncinSa, kuma babu mai bibiyar HukuncinSa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili bushtu Asami السويدية الأمهرية الغوجاراتية القيرقيزية النيبالية اليوروبا الدرية الصومالية المالاجاشية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Banbance banbance mutane a matakan a imani.
  2. An so karfi a ayyuka; Domin yana faruwa ne daga fa'idar abinda ba ya faruwa da rauni.
  3. Mutum ya kamata ya yi kwadayi akan abinda zai anfane shi, kuma ya bar abinda ba zai anfane shi ba.
  4. Yana wajaba akan mumini ya nemi taimakon Allah a dukkanin al'amuransa, kuma kada ya dogara da kansa.
  5. Tabbatar da hukunci da kaddara, kuma shi ba ya kore kokari a sabubba da kokari a neman alkairai.
  6. Hani game da fadin "Da a ce" ta fuskar fushi a lokacin saukar musibu, da haramcin bijirewa hukunci da kaddara ga Allah - Madaukakin sarki -.