عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«مَنْ يُرِدِ اللهُ بِهِ خَيْرًا يُصِبْ مِنْهُ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 5645]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda Allah Yake nufinsa da alheri zai shafeshi da rashin lafiya (zai jarrabeshi)".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5645]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa idan Allah Ya yi nufin wani alheri ga bayinsa muminai sai ya jarrabesu a kawunansu da dukiyoyinsu, don abin da zai faru ga mumini na komawa zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - da addu'a, da kankare munanan ayyuka, da ɗaukaka darajoji.