عن أنس وأبي هريرة رضي الله عنهما مرفوعاً: «لا يُؤْمِنُ أحدُكم حتى أَكُونَ أَحَبَّ إليه مِن وَلَدِه، ووالِدِه، والناس أجمعين».
[صحيح] - [حديث أنس -رضي الله عنه-: متفق عليه. حديث أبي هريرة -رضي الله عنه-: رواه البخاري]
المزيــد ...

Daga Anas da kuma Abu Huraira - Allah ya yarda da su zuwa ga Annabi: "Imanin Dayanku ba zai cika ba har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi daga Dansa da Iyayensa da Mutane baki daya"
Ingantacce ne - Buhari ne ya rawaito shi

Bayani

Manon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi yana bamu labari a cikin wannan Hadisin cewa Imanin Musulmi ba zai cika ba kuma ba zai samu imanin da zai shiga Aljanna ba ba tare da Azaba ba, har sai ya fifita Soyayyar Annabi-tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi-kan son Dansa da Iyayensa da Mutane baki daya wannan kuma cewa Soyayyar Annabi ita ce Soyayyar Allah domin Annabi shi ne Mai isar da sakon Allah kuma mai shiryarwa Izuwa Addininsa kuma soyayyar Allah da Manzonsa ba zata taba inganta ba sai anbi Umarnin Sharia da nisanta duk abunda aka han, Ba wai da rera wakoki ba, ko tarurruka, kidan waka.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin