عَنْ عِيَاضِ بْنِ حِمَارٍ أَخِي بَنِي مُجَاشِعٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَامَ فِينَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ذَاتَ يَوْمٍ خَطِيبًا، فَقَالَ: وَسَاقَ الْحَدِيثَ وَفِيهِ:
«وَإِنَّ اللهَ أَوْحَى إِلَيَّ أَنْ تَوَاضَعُوا حَتَّى لَا يَفْخَرَ أَحَدٌ عَلَى أَحَدٍ، وَلَا يَبْغِي أَحَدٌ عَلَى أَحَدٍ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2865]
المزيــد ...
Daga Iyad ɗan Himar ɗan uwan Mujashi'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu yana mai yin huɗuba, sai ya ce: Sai ya koro hadisin kuma a cikinsa:
«Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai, har kada wani ya yi wa wani alfahari, kuma kada wani ya zalinci wani».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2865]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya miƙe a cikin sahabbansa yana mai huɗuba, ya kasance daga cikin abinda ya ce: Lallai cewa Allah Ya yi masa wahayi cewa ya wajaba akan mutane su yi tawali'u a tsakaninsu, hakan ta hanyar ƙanƙar da kai ga halitta da tausasa lamura, har kada wani ya yi alfahari ta hanyar da'awar girma da kafafa da ɗaukakar da zai danganta kansa ko dukiyarsa ko wanin haka akan wani, kuma kada wani ya zalinci wani, kuma kada ya yi ta'addaci akan wani.