عَنْ سَلْمَانَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنَّ رَبَّكُمْ حَيِيٌّ كَرِيمٌ، يَسْتَحْيِي مِنْ عَبْدِهِ إِذَا رَفَعَ يَدَيْهِ إِلَيْهِ أَنْ يَرُدَّهُمَا صِفْرًا».
[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه] - [سنن أبي داود: 1488]
المزيــد ...
Daga Salman - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lalle Ubangijinku Mai kunya ne kuma Mai karamci ne, Yana jin kunyar bawanSa idan ya ɗaga hannayensa zuwa gare Shi Ya dawo da su babu komai".
[Hasan ne] - - [سنن أبي داود - 1488]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitarwa akan ɗaga hannaye a lokacin addu'a, kuma ya bada labarin cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa (Mai kunya ne) Mai yawan kunya ne, ba Ya barin kyauta, Yana yi wa bawa abinda yake faranta masa, kuma Yana barin abinda yake cutar da shi, (Mai yawan kyauta ne) Yana bayarwa ba tare da tambaya ba to yaya kuma bayan tambaya! Yana jin kunyar bawanSa mumini ya dawo da hannayensa bayan ɗagasu dan yin addu'a babu komai suna babu komai cikinsu a taɓe daga amsawa.