عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَا مِنْ قَوْمٍ يَقُومُونَ مِنْ مَجْلِسٍ لَا يَذْكُرُونَ اللَّهَ فِيهِ إِلَّا قَامُوا عَنْ مِثْلِ جِيفَةِ حِمَارٍ، وَكَانَ لَهُمْ حَسْرَةً».
[صحيح] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 4855]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da ba sa ambaton Allah a cikinsa, face sun tashi kamar mushen jaki, kuma suna masu asara".
[Ingantacce ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 4855]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wasu mutanen da zasu zauna a wani wurin zama sannan su tashi ba su anbaci Allah a cikinsa ba sai sun tashi kamar waɗanda suka taru akan mushen jaki ta ɓangaren ɗoyi da ƙazanta; hakan yayin da suka shagalta a cikin zance daga anbatan Allah, sai wurin zaman ya zama hasara a kansu a ranar alƘiyama da kuma tawaya da dana-sanin da zata lazimcesu.