عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ قَالَ: خَرَجَ مُعَاوِيَةُ عَلَى حَلْقَةٍ فِي الْمَسْجِدِ، فَقَالَ: مَا أَجْلَسَكُمْ؟ قَالُوا: جَلَسْنَا نَذْكُرُ اللهَ، قَالَ آللَّهِ مَا أَجْلَسَكُمْ إِلَّا ذَاكَ؟ قَالُوا: وَاللهِ مَا أَجْلَسَنَا إِلَّا ذَاكَ، قَالَ: أَمَا إِنِّي لَمْ أَسْتَحْلِفْكُمْ تُهْمَةً لَكُمْ، وَمَا كَانَ أَحَدٌ بِمَنْزِلَتِي مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَقَلَّ عَنْهُ حَدِيثًا مِنِّي:
وَإِنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَرَجَ عَلَى حَلْقَةٍ مِنْ أَصْحَابِهِ، فَقَالَ: «مَا أَجْلَسَكُمْ؟» قَالُوا: جَلَسْنَا نَذْكُرُ اللهَ وَنَحْمَدُهُ عَلَى مَا هَدَانَا لِلْإِسْلَامِ، وَمَنَّ بِهِ عَلَيْنَا، قَالَ: «آللَّهِ مَا أَجْلَسَكُمْ إِلَّا ذَاكَ؟» قَالُوا: وَاللهِ مَا أَجْلَسَنَا إِلَّا ذَاكَ، قَالَ: «أَمَا إِنِّي لَمْ أَسْتَحْلِفْكُمْ تُهْمَةً لَكُمْ، وَلَكِنَّهُ أَتَانِي جِبْرِيلُ فَأَخْبَرَنِي أَنَّ اللهَ عَزَّ وَجَلَّ يُبَاهِي بِكُمُ الْمَلَائِكَةَ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2701]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'id AlKudri ya ce: Mu'awiya ya fito ga wata halƙa a cikin masallaci, sai ya ce: Me ya zaunar da ku? suka ce: Mun zauna muna ambatan Allah, ya ce kun rantse da Allah babu abinda ya zaunar da ku sai hakan? suka ce: Wallahi babu abinda ya zaunar da mu sai hakan, ya ce: Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, kuma babu wani a matsayina daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mafi ƙarancin hadisi daga gareni:
Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fito ga wata halƙa daga sahabbansa, sai ya ce; "Me ya zaunar da ku?" suka ce: Mun zauna muna ambatan Allah muna gode masa akan abinda ya shiryar da mu na musulunci, kuma ya yi baiwa da shi garemu, ya ce: "Kun rantse da Allah babu abinda ya zaunar da ku sai hakan? suka ce: Wallahi babu abinda ya zaunar da mu sai hakan, ya ce: "Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai cewa (Mala'ika) Jibril ya zo min sai ya ba ni labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2701]
Mu'awiya Dan Abu Sufyan - Allah Ya yarda da su - ya fito ga wata halƙa a cikin Masallaci, sai ya tambayesu akan wanne abu ne suka taru? sai suka ce: Muna ambatan Allah, sai ya sa suka rantse, Allah Ya yarda da shi - cewa su ba su yi nufin komai da taruwarsu ba sai zikiri, sai suka rantse masa, Sannan ya ce da su: Lallai ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku da kuma kokwanto a gaskiyarku ba, sannan ya bada labari game da matsayinsa ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma cewa shi babu wani mutum dake da matsayin kusancin sa daga gare shi; dan kasancewar Ummu Habiba 'yar uwarsa ce kuma matar annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ce-, dan kuma kasancewarsa daga marubutan wahayi, tare da hakan to shi mai ƙarancin riwaya ne ga hadisai. Sai ya zantar da su cewa annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fito wata rana daga gidansa, sai ya samesu a zaune a cikin masallaci, suna anbaton Allah suna gode masa akan shiryar da su da ya yi , ya kuma ni’imta su da shi, sai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambaye su ya kuma rantsar da su da irin abinda Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - ya aikata tare sahabban sa. Sannan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa musu sababin tambayar sa gare su da kuma rantsar da su da ya yi: Cewa mala'ika Jibrilu - aminci ya tabbata a gare shi - ya zo masa sai ya ba shi labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku, kuma yana bayyanar da falalarku gare su, kuma yana nuna musu kyakkyawan ayyukanku, Yana yabon ku a gurin su.