عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه:
أَنَّ رَجُلًا قَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ إِنَّ لِي قَرَابَةً أَصِلُهُمْ وَيَقْطَعُونِي، وَأُحْسِنُ إِلَيْهِمْ وَيُسِيئُونَ إِلَيَّ، وَأَحْلُمُ عَنْهُمْ وَيَجْهَلُونَ عَلَيَّ، فَقَالَ: «لَئِنْ كُنْتَ كَمَا قُلْتَ، فَكَأَنَّمَا تُسِفُّهُمُ الْمَلَّ وَلَا يَزَالُ مَعَكَ مِنَ اللهِ ظَهِيرٌ عَلَيْهِمْ مَا دُمْتَ عَلَى ذَلِكَ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2558]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa wani mutum ya ce: Ya manzon Allah, ina da wasu 'yan uwa ina sadar musu (da zumunci), su kuma suna yanke mini, ina kyautata musu, su suna munanawa a gareni, ina haƙuri da su, su kuma suna yi min wauta, sai ya ce: "Idan ka kasance kamar yadda ka faɗa, to, kamar kana cusa musu toka mai zafi ne a bakin su, kuma wani mai rinjaye a kansu daga Allah ba zai gushe tare da kai ba muddin dai ka kasance a kan haka".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2558]
Wani mutum ya kai kuka wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi yana da makusanta da 'yan zumunci yana yi musu kyakkyawar mu'amala su kuma suna yi masa kishiyar haka; sai ya sadar da (zumuncin) su ya zo musu alhali su kuma suna yanke masa (zumunci), yana kyautata musu da yin aikin alheri da cika alƙawari su kuma suna munana masa da zalinci da wauta, yana yi musu haƙuri yana yi musu afuwa, su kuma suna yi masa wauta da mummunar magana da mummunan aiki, shin zai ci gaba da sadar musu (da zumunci) tare da abinda aka anbata?
Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: Idan abinda ka faɗa haka yake to lallai cewa kai kana kunyatasu kuma kana wulaƙantasu akan kansu, kamar cewa kai kana ciyar da su toka ce mai zafi; dan yawan kyautatawarka da kuma mummunan aikinsu daga garesu, kuma wani mai taimakonka a kansu daga Allah, kuma mai tunkuɗe maka cutarsu akan abinda ka anbata na kyautatawarka garesu ba zai gushe tare da kai ba, su kuma su ci gaba akan munanawarsu gareka.