عَنْ عُبَيْدِ اللَّهِ بْنِ عَدِيِّ بْنِ الخِيَارِ قَالَ:
أَخْبَرَنِي رَجُلَانِ أَنَّهُمَا أَتَيَا النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي حَجَّةِ الوَدَاعِ وَهُوَ يُقَسِّمُ الصَّدَقَةَ، فَسَأَلَاهُ مِنْهَا، فَرَفَّعَ فِينَا البَصَرَ وَخَفَّضَهُ، فَرَآنَا جَلْدَيْنِ، فَقَالَ: «إِنَّ شِئْتُمَا أَعْطَيْتُكُمَا، وَلَا حَظَّ فِيهَا لِغَنِيٍّ، وَلَا لِقَوِيٍّ مُكْتَسِبٍ».
[صحيح] - [رواه أبو داود والنسائي] - [سنن أبي داود: 1633]
المزيــد ...
Daga Ubaidullahi Ibnu Adi Ibnul Khiyar ya ce:
Wasu mutane biyu sun bani labarin cewa sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Hajjin ban kwana alhali shi yana raba sadaka (zakka), sai suka tambaye shi zakkar, sai ya ɗaga idanuwansa garemu ya kuma yi ƙasa da su, sai ya ganmu ƙarfafa ne, sai ya ce: «Idan kun so zan baku ita, babu rabo a cikinta ga mawadaci, ko ƙaƙƙarfan da yake iya neman na kansa».
[Ingantacce ne] - [رواه أبو داود والنسائي] - [سنن أبي داود - 1633]
Wasu mutane biyu sun zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Hajjin ban kwana, alhali shi yana raba sadaka (zakka), kuma suka nemi ya basu daga cikin zakkar, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sake kallonsu, dan ya gane halinsu, kuma shin ya halatta a basu sadakar ko a'a? Sai ya gansu mazaje ne biyu ƙarfafa, sai ya ce: Idan kuna so zan baku daga cikin zakkar, babu rabo a cikinta ga wanda yake da dukiyar da zata ishe shi, ko ga wanda yake da ikon yin aiki ko juya dukiya, ko da ba shi da dukiyar da za'a ɗauke shi (a matsayin) mawadaci da ita.