عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«تَابِعُوا بَيْنَ الحَجِّ وَالعُمْرَةِ، فَإِنَّهُمَا يَنْفِيَانِ الفَقْرَ وَالذُّنُوبَ كَمَا يَنْفِي الكِيرُ خَبَثَ الحَدِيدِ، وَالذَّهَبِ، وَالفِضَّةِ، وَلَيْسَ لِلْحَجَّةِ الْمَبْرُورَةِ ثَوَابٌ إِلاَّ الجَنَّةُ».
[صحيح] - [رواه الترمذي والنسائي وأحمد] - [سنن الترمذي: 810]
المزيــد ...
An karbo daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ku bibiyi tsakanin Hajji da Umarah, domin cewa su suna kore talauci da kuma zunubai kamar yadda zugazagi yake kore dattin ƙarfe, da zinariya, da azirfa, kuma kuɓutaccen Hajji ba shi da wani sakamako sai aljanna".
[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 810]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan kusantowa tsakanin yin ibadun Hajji da kuma yin Umarah da rashin yankewa daga yinsu tare da iko, domin cewa yin su yana zama sababi na kawar da talauci da zunubai da kuma tasirinsu a cikin zuciya, kamar yadda zugazugi na wuta yana zamowa sababi a cikin kawar da dattin ƙarfe da abinda yake cakuɗuwa da shi na ma'adanan da su ba daga gare shi suke ba.