عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَوْ يَعْلَمُ النَّاسُ مَا فِي النِّدَاءِ وَالصَّفِّ الْأَوَّلِ ثُمَّ لَمْ يَجِدُوا إِلَّا أَنْ يَسْتَهِمُوا عَلَيْهِ لَاسْتَهَمُوا، وَلَوْ يَعْلَمُونَ مَا فِي التَّهْجِيرِ لَاسْتَبَقُوا إِلَيْهِ، وَلَوْ يَعْلَمُونَ مَا فِي الْعَتَمَةِ وَالصُّبْحِ لَأَتَوْهُمَا وَلَوْ حَبْوًا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 437]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Da a ce mutane suna sanin abinda ke cikin kiran sallah (na lada) da kuma sahu na farko sannan ba za su samu ba sai idan sun yi ƙuri'a a kansa da sun yi ƙuri'a, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin gaggawa (zuwa sallah a farkon lokaci) da sun yi gasar zuwa gare shi, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin sallar dare (Issha) da Asuba da sun zo musu koda da jan ciki ne».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 437]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mutane da a ce suna sanin abinda ke cikin kiran sallah da sahun farko na falala da alheri da albarka sannan ba za su samu damar samun shi ba sai sun yi ƙuri'a akan sa, waye a cikinsu ya fi cancanta akan ɗan uwansa ? da sun yi ƙuri'a, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin gaggawa zuwa sallah a farkon lokacinta da sun yi rigegeniya gareta, kuma da a ce suna sanin gwargwadan lada a zuwa sallar Issha'i da sallar Asuba da zuwa gare su ya yi sauƙi koda da jan ciki ne akan gwiwowi kamar yadda yaro yake tafiya a farkon al'amarinsa.