+ -

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«أَتِمُّوا الصَّفَّ المُقَدَّمَ، ثُمَّ الَّذِي يَلِيهِ، فَمَا كَانَ مِنْ نَقْصٍ فَلْيَكُنْ فِي الصَّفِّ المُؤَخَّرِ».

[صحيح] - [رواه أبو داود والنسائي] - [سنن أبي داود: 671]
المزيــد ...

Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Ku cika sawun gaba, sannan wanda ke biye da shi, abin da aka samu tawaya daga gare shi to ya zama a cikin sawun ƙarshe ne».

[Ingantacce ne] - [رواه أبو داود والنسائي] - [سنن أبي داود - 671]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci mazaje masu yin sallah a jam'i da cika sawun farko, sannan da cika sawun da ke biye da shi, idan za’a samu wata tawaya a cikin wani sawu to wannan tawayar ta zama a sawun ƙarshe ne.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin sunna a kan daidaita sawu.
  2. Ya wajaba akan masallata kada su bar tawaya a cikin sawun gaba, kai tawaya ta zama a cikin sawun ƙarshe ne.
Fassara: Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Vietnam Kurdawa Portuguese Swahili Yaran Tailand Asami الهولندية الدرية المجرية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin