عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صلَّى اللَّهُ عليْه وسلَّمَ، قَالَ:
«إِذَا أُقِيمَتِ الصَّلَاةُ فَلَا صَلَاةَ إلَّا المَكْتُوبَةُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 710]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Idan an tsaida sallah to babu wata sallah sai ta farilla kawai».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 710]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda yake cikin masallaci ya fara yin sallar nafila bayan an yi iƙamar sallar farilla.