عن عبد الله بن عُمر وأبي هريرة رضي الله عنهما أنهما سمعا رسول الله صلى الله عليه وسلم، يقول على أعواد منبره:
«لَيَنْتَهِيَنَّ أَقْوَامٌ عَنْ وَدْعِهِمُ الْجُمُعَاتِ أَوْ لَيَخْتِمَنَّ اللهُ عَلَى قُلُوبِهِمْ، ثُمَّ لَيَكُونُنَّ مِنَ الْغَافِلِينَ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 865]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Umar da kuma Abu Huraira - Allah Ya yarda da su - cewa su sun ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - yana faɗa akan minbarinsa:
"Lallai wasu mutane kodai su hanu daga barin Juma'o'i, ko Allah Zai yi yumƙi akan zukatansu, sannan zasu kasance daga marafkana"
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 865]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kan mimbari ya yi gargaɗi daga barin sallar Juma'a da zama na kin zuwa ba tare da wani uzuri ba, dan wulaƙantarwa da kuma kasala, ko Allah Ya yi yumƙi akan zukatansu Ya rufesu kuma Ya sanya kariyar da zai hanasu bin gaskiya, sannan zasu kasance daga rafkanannu daga sabubban alheri, mai korewa rayukansu ayyukan ɗa'a.