عَنْ أَبِي الْجَعْدِ الضَّمْرِيِّ رَضيَ اللهُ عنهُ، وَكَانَتْ لَهُ صُحْبَةٌ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ تَرَكَ ثَلَاثَ جُمَعٍ تَهَاوُنًا بِهَا طَبَعَ اللَّهُ عَلَى قَلْبِهِ».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 1052]
المزيــد ...
Daga Abul Ja'ad al-Damri - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance sahabi ne, cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ya bar Juma'o'i uku dan wulaƙantar da su Allah zai yi yumƙi akan zuciyarsa".
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 1052]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga barin sallar Juma'a, kuma wanda ya bar sallar Juma'a sau uku dan sakaci da kasawa ba tare da wani uzuri ba Allah zai rufe zuciyarsa ta hanyar hana isar alheri gare shi .