عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنِينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا أَنَّهَا قَالَتْ:
يَا رَسُولَ اللَّهِ، نَرَى الجِهَادَ أَفْضَلَ العَمَلِ، أَفَلاَ نُجَاهِدُ؟ قَالَ: «لَا، لَكُنَّ أَفْضَلُ الجِهَادِ: حَجٌّ مَبْرُورٌ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 1520]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Ya manzon Allah, muna ganin yaƙi shi ne mafificin aiki, shin ba ma yi yaƙi ba? ya ce: "A'a, sai dai mafificin yaƙi: Shi ne kubutaccen aikin Hajji".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1520]
Sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun kasance suna ganin yaƙi a tafarkin Allah da yakar maƙiya yana daga mafifitan ayyuka, sai Nana A'isah - Allah Ya yarda da ita - ta tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa zasu iya yin yaƙi?
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nuna musu mafificin yaƙi a cikin haƙƙinsu shi ne kubutaccen aikin Hajji wanda ya dace da AlKur'ani da Sunnah, wanda ya kubuta daga zunubi da kuma riya.