عَنْ سَفِينَةَ رَضيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ:
كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُغَسِّلُهُ الصَّاعُ مِنَ المَاءِ مِنَ الجَنَابَةِ، وَيُوَضِّئُهُ المُدُّ.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 326]
المزيــد ...
Daga Safina - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance Sa’i ɗaya na ruwa yana isarsa a wankan tsarki, kuma musun Nabiy ɗaya yana isarsa a alwala.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 326]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wankan tsarki da sa’i ɗaya, kuma yana alwala da mudun Nabiy ɗaya. Sa'i: Mudun Nabiy haɗu ne, mudun Nabiy kuma: Gwargwadan cikin tafuka biyu na mutum madaidaicin halitta.