عَنْ إِبرَاهِيمَ النَّخَعِيِّ عَنْ هَمَّامِ بنِ الحَارِثِ قَالَ:
بَالَ جَرِيرٌ، ثُمَّ تَوَضَّأَ، وَمَسَحَ عَلَى خُفَّيْهِ، فَقِيلَ: تَفْعَلُ هَذَا؟ فَقَالَ: نَعَمْ، رَأَيْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَالَ، ثُمَّ تَوَضَّأَ وَمَسَحَ عَلَى خُفَّيْهِ. قَالَ الأَعْمَشُ: قَالَ إِبْرَاهِيمُ: كَانَ يُعْجِبُهُمْ هَذَا الحَدِيثُ؛ لِأَنَّ إِسْلَامَ جَرِيرٍ، كَانَ بَعْدَ نُزُولِ المَائِدَةِ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 272]
المزيــد ...
Daga Ibrahim al-Nakha'i daga Hammam Ibnul Haris ya ce:
Jarir ya yi fitsari, sannan ya yi alwala ya yi shafa akan huffinsa, sai aka ce: Ya kake yin haka? ya ce: Eh, Na ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi fitsari, sannan ya yi alwala kuma ya yi shafa akan huffinsa. Al-A'amash ya ce: Ibrahim ya ce: Wannan hadisin yana ƙayatar da su; domin musuluntar Jarir, ta kasance ne bayan saukar (Suratul) Ma'idah.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 272]
Jarir Ibnu Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya yi fitsari sannan ya yi alwala, kuma hakan ya wadatar da yin shafa akan huffinsa bai wanke ƙafafunsa ba, sai wanda ke gefensa Ya ce masa: Ya kake aikata haka?! sai ya ce: Eh, na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi fitsari, sannan ya yi alwala kuma ya yi shafa akan huffinsa. Jarir ya kasance ya musulunta daga baya-baya, bayan saukar Suratul Ma'idah wacce a cikinta ne ayar alwala take, yana mai nuni da hakan zuwa ga shafa akan huffi ba'a shafe hukuncin sa ba a wannan ayar.