Karkasawa:
+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ صَخْرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْت رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم يَقُولُ:
«مَا نَهَيْتُكُمْ عَنْهُ فَاجْتَنِبُوهُ، وَمَا أَمَرْتُكُمْ بِهِ فَافْعَلُوا مِنْهُ مَا اسْتَطَعْتُمْ، فَإِنَّمَا أَهْلَكَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ كَثْرَةُ مَسَائِلِهِمْ، وَاخْتِلَافُهُمْ عَلَى أَنْبِيَائِهِمْ».

[صحيح] - [رواه البخاري ومسلم] - [الأربعون النووية: 9]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
«Duk abin da na haneku daga gare shi to ku nisance shi, kuma abinda na umarce ku da shi to ku zo da shi dai dai iyawarku, domin abin da ya halaka magabatanku (shi ne) yawan tambayoyinsu da kuma saɓawarsu ga Annabawansu».

-

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana mana cewa shi idan ya hana mu wani abu to ya wajaba a kanmu mu nisance shi, ba tare da togaciya ba, idan kuma ya umarce mu da wani abu to wajibi ne a kanmu mu aikata abin da zamu iya daga gare shi. Sannan ya gargaɗemu dan kar mu zama kamar wasu daga cikin al'ummun da suka gabata lokacin da suka yawaita tambayoyi ga Annabawan su tare da saɓa wa annbawan, sai Allah Ya yi musu uƙuba da nau'ikan halaka da rusawa, to yana kamata kada mu zama irinsu dan kada mu halaka kamar yadda suka halaka.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hadisin ƙa'ida ne akan bayanin wajibi domin aikata abinda aka yi umarni da kuma nisantar abin da aka hana.
  2. Hani, ba’a yi rangwami akan aikata wani abu daga gare shi ba, umarni kuma an ƙayyade shi da gwargwadan iko; domin bari abin ƙaddarawa ne, aiki kuma yana buƙatuwa zuwa ga iko akan samar da aikin da aka yi umarni da shi.
  3. Abin da aka hana yana ƙunsar kaɗan da mai yawa; domin nisantarsa ba ya yi wu wa sai da nisantar ƙanƙaninsa da mai yawansa, misali: Ya hanemu daga riba to hanin ya ƙunshi ƙanƙaninta da kuma mai yawanta.
  4. Barin sabubban da zasu iya kaiwa zuwa ga haram; domin hakan yana daga ma'anar nisanta.
  5. Ba ya kamata ga mutum idan ya ji umarnin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce ba: Shin wajibi ne ko mustahabbi ne, kawai ya wajaba a kansa ya yi gaggawa zuwa aikata shi; saboda faɗinsa: «Ku zo da shi gwargwadan iyawarku».
  6. Yawan tambayoyi sababi ne na halaka musamman ma a cikin al'amuran da ba zai yi wu akai zuwa garesu ba, misali mas'alolin gaibu, da siffar yanayin ranar alƙiyama, kada ka yawaita tambaya a cikinsu sai ka halaka, sai ka zama mai tsanantawa a cikin Addini mai zirfafawa.
Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Turkiyanci Rashanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci الأمهرية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الدرية الصربية الطاجيكية Kinyarwanda المجرية التشيكية الموري Kanadische Übersetzung الولوف Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية الجورجية المقدونية الخميرية
Manufofin Fassarorin
kashe kashe
Kari