عَنْ أَبِي رُقَيَّةَ تَمِيمِ بْنِ أَوْسٍ الدَّارِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«الدِّينُ النَّصِيحَةُ» قُلْنَا: لِمَنْ؟ قَالَ: «لِلهِ وَلِكِتَابِهِ وَلِرَسُولِهِ وَلِأَئِمَّةِ الْمُسْلِمِينَ وَعَامَّتِهِمْ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [الأربعون النووية: 7]
المزيــد ...
Daga Abu Ruƙayya Tamim ibnu Aws al-Dari - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Addini nasiha ne" Muka ce; ga wa? Ya ce; "Ga Allah da littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin musulmai da dukkaninsu".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [الأربعون النووية - 7]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa Addini a tsaye yake a kan ikhlasi da gaskiya, har sai an yi shi kamar yadda Allah Ya wajabta, cikakke ba tare da tawaya ko algus ba. Sai aka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Ga wa nasihar za ta kasance? sai ya ce: Na farko: Nasiha ga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -: ta hanyar tsarkake aiki gare shi, da rashin haɗa Shi da wani, kuma mu yi imani da RububiyyarSa da UluhiyyarSa da sunayenSa da siffofinSa, da girmama umarninSa, da kira zuwa ga imani da Shi. Na biyu: Nasiha ga littafinSa shi ne AlKur'ani mai girma: Shi ne mu ƙudirce cewa shi zancenSa ne, kuma ƙarshen littattafanSa, kuma shi mai shafewa ne ga dukkanin shari'o'in da suke kafinsa, kuma mu girmama shi, mu karanta shi haƙiƙanin karanta shi, mu yi aiki da muhkam ɗinsa, kuma mu miƙa wuya ga masu kamanceceniya daga gare shi, kuma mu kore tawilin masu karkace masa, mu wa'azantu da wa'azozinsa, da yaɗa ilimummukansa, mu yi kira zuwa gare shi. Na uku: Nasiha ga ManzonSa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Shi ne mu ƙudire cewa shi ne ƙarshen Manzanni, mu gasgata shi a cikin abin da ya zo da shi, mu yi riko da umarninsa, mu nisanci haninsa, kuma kada mu bautawa Allah da komai sai abin da ya zo da shi, mu girmama haƙƙinsa, mu girmama shi, mu yaɗa Da'awarsa, mu yaɗa shari'arsa, kuma mu kore tuhuma daga gare shi. Na huɗu: Nasiha ga shugabannin musulmai: Ta hanyar taimakonsu a kan gaskiya, da rashin jayayya da su a al'amari, da ji da biyayya garesu akan biyayya ga Allah. Na biyar: Nasiha ga musulami: Ta hanyar kyautatawa zuwa garesu da kiransu, da hana cutar da su, da son alheri garesu, da taimakekeniya tare da su a kan biyayya da tsoron Allah.