+ -

عَنْ حُذَيْفَةَ بْنِ اليَمَانِ رَضيَ اللهُ عنه:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ إِذَا أَرَادَ أَنْ يَنَامَ وَضَعَ يَدَهُ تَحْتَ رَأْسِهِ، ثُمَّ قَالَ: «اللَّهُمَّ قِنِي عَذَابَكَ يَوْمَ تَجْمَعُ أَوْ تَبْعَثُ عِبَادَكَ».

[صحيح] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 3398]
المزيــد ...

Huzaifa Ibnul Yaman -Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin yin bacci yana sanya hannunsa ƙarƙashin kansa, sannan ya ce: «‌Ya Allah Ka kareni azabarKa ranar da zaKa tara ko zaka tashi bayinKa».

[Ingantacce ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi] - [سنن الترمذي - 3398]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya kwanta dan yayi barci, sai ya shimfiɗa hannunsa na dama kuma ya sanya kundukukinsa (kumatunsa)na dama akansa, sai ya ce: «‌Ya Allah» Ubangijina «‌Ka kareni» Ka kiyayeni daga «‌azabarKa» da uƙubarKa «‌ranar da zaKa tara ko zaKa tashi bayinKa» a ranar hisabi, ranar alƙiyama.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar wannan addu'ar mai albarka, kuma an so kiyayewa a kanta dan yin koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  2. An so kwanciya akan ɓarin jiki na dama.
  3. Sindi ya ce: Faɗinsa (Ya Allah Ka kareni azabarKa), a cikinsa cewa yana kamata ga mai hankali ya maida baccinsa tsani dan tina mutuwa da kuma tashi a bayanta.
  4. Kariya daga azabar Allah a ranar alƙiyama tana kasancewa ne da falalar Allah da kuma rahamarSa, ta hanyar dacewar bawa ga aiki na gari da kuma gafarar Allah ga bayinSa.
  5. Tawali'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa kuma Majiɓincin al'amuransa - Allah Maɗaukakin sarki -.
  6. Tabbatar da taruwa da kuma makoma, kuma cewa mutane masu komawa ne zuwa ga Ubangijinsu dan ya yi musu hisabi akan ayyukansu, wanda ya samu alheri to ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki -, wanda ya samu koma bayan haka to kada ya zargi kowa sai kansa, kawai su ne ayyukan bayi Allah Yana kiyaye musu su.
  7. Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan bayanin halayen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agagre shi - a baccinsa.
  8. Faɗinsa: "Sai ya sanya hannunsa na dama ƙarƙashin kundukukinsa" ya kasance daga al'adunsa - tsra da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne damantawa a cikin kowane abu, sai dai abinda dalili ya zo akan saɓaninsa.
  9. Bacci akan ɓarin jiki na dama ya fi saurin farkawa saboda rashin tabbatar zuciya a cikin wannan halin, kuma ya fi sauƙi ga zuciya; domin ita zuciya a ɓangaren hagu take, da a ce bawa ya yi bacci akan ɓarin hagu zai cutar da zuciya dan nauyin gaɓɓai a kanta.
Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Yaran Tailand Asami الأمهرية الدرية الرومانية المجرية الجورجية الخميرية الماراثية
Manufofin Fassarorin