عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِذَا دَخَلَ أَحَدُكُمْ المَسْجِدَ فَلْيُسَلِّمْ عَلَى النَّبِيِّ وَلْيَقُلْ: اللَّهُمَّ افْتَحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ، وَإِذَا خَرَجَ فَلْيُسَلِّمْ عَلَى النَّبِيِّ وَلْيَقُلْ: اللَّهُمَّ اعْصِمْنِي مِنْ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ»، وَلِلْحَاكِمِ: «وَإِذَا خَرَجَ فَلْيُسَلِّمْ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَلْيَقُلْ: اللَّهُمَّ أَجِرْنِي مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ».
[حسن] - [رواه ابن ماجه والحاكم] - [سنن ابن ماجه: 773]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
«Idan ɗayanku ya shiga masallaci to ya yi wa Annabi salati kuma ya ce: Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa, idan kuma zai fita to ya yi wa Annabi sallama sannan ya ce: Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa». (Riwayar) Hakim: «Idan zai fita to ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sallama, sannan ya ce: Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa».
[Hasan ne] - [رواه ابن ماجه والحاكم] - [سنن ابن ماجه - 773]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da musulmi cewa idan ya yi nufin shiga masallaci ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - salati da faɗinsa: Ya Allah Ka yi tsira Ka yi aminci ga (Annabi) Muhammad, sannan ya ce: (Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa). Idan zai fita to ya yi wa Annabi salati sai ya ce: (Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa). A cikin riwayar Hakim: Sai ya ce: (Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa).