+ -

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ صَلَّى صَلاَتَنَا وَاسْتَقْبَلَ قِبْلَتَنَا وَأَكَلَ ذَبِيحَتَنَا فَذَلِكَ المُسْلِمُ الَّذِي لَهُ ذِمَّةُ اللَّهِ وَذِمَّةُ رَسُولِهِ، فَلاَ تُخْفِرُوا اللَّهَ فِي ذِمَّتِهِ».

[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 391]
المزيــد ...

Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Wanda ya sallaci irin sallarmu kuma ya fuskanci alƙiblarmu, kuma ya ci yankanmu to wannan shine muslmin da yake da alƙawarin Allah da alƙawarin ManzonSa, dan haka kada ku warware alƙawarin Allah».

[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 391]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya lazimci shari'un addini na zahiri cewa ya yi irin sallarmu, kuma ya fuskanci alƙiblarmu, kuma ya ci yankanmu yana mai halatta shi ; to wannan shine musulmin da yake da amanar Allah da ManzonSa da kuma alƙawarinSa, dan haka kada ku warware amanar Allah da alƙawarinSa a cikinsa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Ibnu Rajab ya ce: Wannan hadisin ya yi nuni akan cewa jini ba ya zama abin tsarewa da mujarradin shahada biyu, har sai ya tsaya da haƙƙoƙinsu, kuma mafi ƙarfin haƙƙoƙinsu ita ce sallah; saboda haka ne ta keɓanceta da ambato, a cikin wani hadisin daban ya raɓa zakka zuwa ga sallah.
  2. Al'amarin mutane abin ɗauka ne akan zahiri banda baɗini, wanda ya bayyanar da alamomin addini za'a gudanar da hukunce-hukuncen Musulmai a kansa muddin dai bai gudanar da saɓanin hakan ba.
  3. Ibnu Rajab ya ce: Ambatan fuskantar alƙibla nuni ne zuwa cewa babu makawa da zuwa da sallar musulmai wacce aka shara'anta a cikin littafinsu wanda aka saukar ga annabinsu ita ce sallah da fuskantar Ka'aba, inba haka bafa wanda ya yi sallah zuwa Baitul Maƙdisi bayan anshafeta kamar Yahudawa ko kallan gabas kamar Nasara to ba musulmi ba ne, koda ya yi shaidar tauhidi.
  4. A cikinsa akwai dalili akan girman gurin fuskantar alƙibla a sallah, domin cewa a cikin sharuɗɗan sallah bai ambaci waninta ba, kamar tsarki da waninsa.
  5. Ibnu Rajab ya ce: Amabatansa cin yankan musulmai a cikinsa akwai nuni zuwa cewa babu makawa daga lazimtar dukkanin shari'un musulunci na zahiri, kuma mafi girmansu shine cin yankan musulmai, da kuma dacewa da su a cikin yankansu, duk wanda ya hanu daga hakan to ba musulmi ba ne.
Fassara: Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Vietnam Kurdawa Portuguese Swahili Yaran Tailand Asami الهولندية الدرية المجرية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin