عَنْ عُقْبَةَ بْنِ عَامِرٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ لِي رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«أُنْزِلَ -أَوْ أُنْزِلَتْ- عَلَيَّ آيَاتٌ لَمْ يُرَ مِثْلُهُنَّ قَطُّ، الْمُعَوِّذَتَيْنِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 814]
المزيــد ...
Daga Uƙubah Ibnu Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce mini:
«An saukar min da wasu ayoyi (waɗanda) ba'a taɓa ganin kwatankwacinsu ba ko sau ɗaya, Falaƙi da Nasi».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 814]
Uƙbah ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: A daren nan Allah Ya saukar min da wasu ayoyi ba'a taɓa ganin kwatankwacinsu ba - wato a neman tsari (Dafa'i) - sune A'uzai guda biyu: Surar {Ƙul A'uzau bi rabbil falaƙ}, da surar {Ƙul A'uzu bi rabbin Nas}.