عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَا تَمْنَعُوا إِمَاءَ اللَّهِ مَسَاجِدَ اللَّهِ، وَلَكِنْ لِيَخْرُجْنَ وَهُنَّ تَفِلَاتٌ».
[حسن] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 565]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
«Kada ku hana bayin Allah mata (zuwa) masallatan Allah, saidai su fita alhali ba su yi mummunar shiga ba».
[Hasan ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 565]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana majiɓincin al'amarin mace da wanda ke kula da ita game da hana mata zuwa masallatai, kuma ya umarci mata in zasu fita su fita ba tare da sun shafa tirare ba, kuma ba tare da sun yi mummunar shiga ba; dan kar su zama sababi a fitinar maza.