عَنْ هِشَامِ بْنِ حَكِيمِ بْنِ حِزَامٍ رَضيَ اللهُ عنهما أَنَّهُ مَرَّ عَلَى أُنَاسٍ مِنَ الْأَنْبَاطِ بِالشَّامِ، قَدْ أُقِيمُوا فِي الشَّمْسِ، فَقَالَ: مَا شَأْنُهُمْ؟ قَالُوا: حُبِسُوا فِي الْجِزْيَةِ، فَقَالَ هِشَامٌ: أَشْهَدُ لَسَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«إِنَّ اللهَ يُعَذِّبُ الَّذِينَ يُعَذِّبُونَ النَّاسَ فِي الدُّنْيَا».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2613]
المزيــد ...
Daga Hisham Ibnu Hakim Ibnu Hizam - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya wuce wasu mutane daga cikin manoma a Sham, haƙiƙa an tsaida su a cikin rana, sai ya ce: Meke damunsu? suka ce: Antsaresu ne saboda jizya, sai Hisham ya ce: Na shaida cewa na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
«Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2613]
Hisham Ibnu Hakim Ibnu Hizam - Allah Ya yarda da su - ya wuce wasu manoma daga baubayi a Sham, an tsayar da su a zafin rana, sai ya yi tambaya game da lamarinsu? Sai aka ba shi labarin cewa su an aikata musu haka ne saboda basu bada (jizya ba) alhali su suna da ikon hakan. Sai Hisham - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ina shaida cewa na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya akan zalinci ba tare da wani haƙƙi ba.