عَنْ قَتَادَةَ قَالَ:
سُئِلَ أَنَسٌ كَيْفَ كَانَتْ قِرَاءَةُ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ؟ فَقَالَ: «كَانَتْ مَدًّا»، ثُمَّ قَرَأَ: {بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ} [الفاتحة: 1] يَمُدُّ بِبِسْمِ اللَّهِ، وَيَمُدُّ بِالرَّحْمَنِ، وَيَمُدُّ بِالرَّحِيمِ.
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 5046]
المزيــد ...
Daga Ƙatada ya ce:
An tambayi Anas yaya karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake? sai ya ce: «Ya kasance yana yin madda», sannan ya karanta: {Bismillahir rahmanir rahim}[al-Fatiha:1] yana yin maddar Bismillah, kuma yana yin maddar Al-Rahman, kuma yana yin maddar Al-Rahim.
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5046]
An tambayi Anas ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - yaya karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - na Alƙur'ani yake? sai ya ce: Ya kasance yana jan sautinsa da karatu ja; yana jan Lami kafin Ha'i na lafazin jalalah, kuma yana jan Mim wanda ke kafin Nun daga Al-Rahman, kuma yana jan Ha'i daga Al-Rahim.