عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَا مِنَ الأَنْبِيَاءِ نَبِيٌّ إِلَّا أُعْطِيَ مَا مِثْلهُ آمَنَ عَلَيْهِ البَشَرُ، وَإِنَّمَا كَانَ الَّذِي أُوتِيتُ وَحْيًا أَوْحَاهُ اللَّهُ إِلَيَّ، فَأَرْجُو أَنْ أَكُونَ أَكْثَرَهُمْ تَابِعًا يَوْمَ القِيَامَةِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4981]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
«Babu wani Annabi daga cikin Annabawa face an ba shi daga cikin ayoyi waɗanda mutane za su yi imani da shi, ni kuma abin da aka bani shi ne wahayi da Allah Ya yi mini wahayi ina fatan na fisu mabiya ranar alƙiyama».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4981]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa Annabawa dukkaninsu Allah Ya ƙarfafesu kuma Ya basu ayoyi da mu'ujizoji waɗanda suka saɓawa al'adu waɗanda ake kafa hujja da su akan Annabtarsu, kuma suna hukunta imanin wanda ya gansu ya gasgatasu, kuma cewa shi abin rinjaye ne a kansa a cikin kalubalantar inda ba zai iya tunkuɗesu ba akan kansa, sai dai zai iya musantasu kuma ya yi tsaurin kai. Kawai shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ayarsa da mu'ujizarsa ita ce Alƙur'anin da Allah Ya yi masa wahayinsa; saboda abin da ya ƙunsa na gajiyarwa mabayyaniya tabbatacciya saboda yawan fa'idarsa da kuma gamewar amfaninsa, dan abin da ya ƙunsa akan Da’awah da hujja da kuma bada labarin abin da zai kasance, sai amfaninsa ya game wanda ya halarta da wanda baya nan da wanda aka samu da wanda za'a samu, sannan ya ce: Ina fatan in zama na fisu yawan mabiya a ranar alƙiyama.