+ -

عَنِ ابْنِ أَبِي مُلَيْكَةَ:
عَنْ بَعْضِ أَزْوَاجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -قَالَ: أَبُو عَامِرٍ، قَالَ نَافِعٌ: أُرَاهَا حَفْصَةَ- أَنَّهَا سُئِلَتْ عَنْ قِرَاءَةِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَتْ: إِنَّكُمْ لَا تَسْتَطِيعُونَهَا قَالَ: فَقِيلَ لَهَا أَخْبِرِينَا بِهَا. قَالَ: فَقَرَأَتْ قِرَاءَةً تَرَسَّلَتْ فِيهَا قَالَ أَبُو عَامِرٍ: قَالَ نَافِعٌ: فَحَكَى لَنَا ابْنُ أَبِي مُلَيْكَةَ {الحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ} [الفاتحة: 2] ثُمَّ قَطَّعَ {الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ} [الفاتحة: 1] ثُمَّ قَطَّعَ {مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ}.

[صحيح] - [رواه أحمد] - [مسند أحمد: 26470]
المزيــد ...

Daga Ibnu Abi Mulaikah:
Daga wata daga cikin matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Abu Amir ya ce: Nafi'u Ya ce: Ina zatan Nana Hafsa ce - Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Lallai ku ba zaku iya ba, ya ce: Sai aka ce mata bamu labarin yadda karatun yake. Ya ce: Sai ta yi karatun da ta yi a sake, Abu Amir ya ce: Nafi'u ya ce: Sai Ibnu Abi Mulaikah ya hakaito mana {Alhamdu lillahi rabbil Aalamin} [al-Fatiha: 2]. sannan ya yanyanke {Al-rahmanur Rahim} [al-Fatiha: 1] sannan ya yanyanke {Maliki yaumud din}.

[Ingantacce ne] - [Ahmad ne ya rawaito shi] - [مسند أحمد - 26470]

Bayani

An tambayi Nana Hafsa uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -: Yaya Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake karanra Alƙur'ani? Sai ta ce: Lallai ku ba zaku iya irin nasa ba, sai aka ce mata; Faɗa mana. Nafi'u ya ce sai Ibnu Abi Mulaikah ya karanta karatun da yayi shi a hankali; dan ta hakaito kuma ta kusanto musu da yadda karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ke, sai ya karanta: {Alhamdu lillhi rabbil Aalamin} sannan ya yanyanke karatun, {Arrahmanur rahim}, sannan ya yanyanke karatun, {Maliki yaumid din}.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin karatun Alƙur'ani.
  2. Ɗabbaƙawa na ilimi na bayanin kaifiyyar karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. Halaccin yin karatu a hankali kuma hakan ya fi kusanto da Tadabburin ma'anoninsa.
  4. Himmatuwar magabata na gari da Alƙur'ani mai girma da kuma aikin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  5. Muhimmancin sanin Tajwidi da kuma Ulumul Ƙur'an.
Fassara: Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Vietnam Kurdawa Portuguese Yaran Tailand Asami الهولندية الدرية المجرية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin