+ -

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ:
اعْتَكَفَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي المَسْجِدِ، فَسَمِعَهُمْ يَجْهَرُونَ بِالقِرَاءَةِ، فَكَشَفَ السِّتْرَ، فَقَالَ: «أَلَا إِنَّ كُلَّكُمْ مُنَاجٍ رَبَّهُ، فَلَا يُؤْذِيَنَّ بَعْضُكُمْ بَعْضًا، وَلَا يَرْفَعْ بَعْضُكُمْ عَلَى بَعْضٍ فِي القِرَاءَةِ»، أَوْ قَالَ: «فِي الصَّلَاةِ».

[صحيح] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 1332]
المزيــد ...

Daga Abu Sa'id al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi i'itikafi a cikin Masallaci, sai ya ji su suna bayyanar da karatu, sai ya yaye mayafi, sai ya ce: «Ku saurara, lallai kowannenku yana ganawa ne da Ubangijinsa, dan haka kada sashinku ya cutar da sashi, kada kuma sashinku ya ɗaga muryarsa ga sashi a cikin karatu», ko cewa ya yi: «A cikin sallah».

[Ingantacce ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 1332]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana zaune yana i'itikafi a cikin wata ƙubba a cikin Masallacinsa dan neman kusanci ga Allah, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ji sahabbansa suna bayyanar da karatun Alƙur'ani a bayyane mai tsanani sashinsu yana cutar da sashi. Sai ya yaye mayafi daga ƙubbar, ya zargi wanda ya aikata haka ya zarge shi, sai ya ce: Dukkaninku kuna ganawa ne da Ubangijinku ta hanyar karatun Alƙur'ani, dan haka kada sashinku ya cutar da sashi, kuma kada sashinku ya ɗaga muryarsa akan sashi a cikin karatu, ko a cikin sallah.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani akan ɗaga murya a karatun Alƙur'ani, idan ya kasance a akwai cutarwa ga wani a cikinsa.
  2. Koyarwar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sahabbansa ladubann karartun Alƙur'ani.
Fassara: Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Vietnam Kurdawa Portuguese Yaran Tailand Asami الهولندية الدرية المجرية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin