+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مِنْ حُسْنِ إِسْلَامِ المَرْءِ تَرْكُهُ مَا لَا يَعْنِيهِ».

[قال النووي: حديث حسن] - [رواه الترمذي وغيره] - [الأربعون النووية: 12]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Yana daga kyan Musuluncin mutum yabar abin da babu ruwansa».

[قال النووي: حديث حسن] - [رواه الترمذي وغيره] - [الأربعون النووية - 12]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga cikar kyawun Musuluncin musulmi da kuma cikar imaninsa, ya nisanci abin da bai shafe shi ba, kuma bai keɓance shi ba, bai da alaƙa da shi da kuma abin da ba zai amfane shi ba na maganganu da ayyuka, ko kuma abin da baruwansa da shi na al'amuran Addini da duniya, shagaltuwa da abin da bai shafi mutum ba wataƙila zai shagaltar da shi daga abin da akwai ruwansa a ciki, ko ya kai shi zuwa ga bin da nisantarsa yake wajaba akansa; domin kuwa mutum abin tambaya ne game da ayyukansa a ranar lahira.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Mutane mabanbanta ne a Musulunci, kuma shi yana ƙara kyau saboda wasu daga cikin ayyuka.
  2. Barin maganagnu marasa anfani da ayyuka dalili ne akan cikar Musuluncin mutum.
  3. Kwaɗaitarwa akan shagltuwa a kan abin da ya shafi mutum na sha'anin Addininsa da duniyarsa, idan yana daga kyan Musuluncin mutum ya bar abin da bai shafe shi ba, to yana daga kyawunsa ya shagaltu a cikin da ya shafe shi .
  4. Ibnul Ƙayyim - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tattaro tsantseni gabaɗayansa a cikin kalma ɗaya, sai ya ce: «Yana daga kyan Musuluncin mutum ya bar abinda babu ruwansa» to wannan ya game barin abin da bai shafe shi ba: Na magana, da kallo, da sauraro, da kamu, da tafiya, da tinani, da sauran motsi na zahiri da na baɗini, wannan ita ce kalma mai warkarwa a cikin tsantseni.
  5. Ibnu Rajab ya ce; Wannan hadisin asali ne na tushen ladabi.
  6. Kwaɗaitarwa akan neman ilimi; domin da shi ne mutum yake sanin abin da ya shafe shi da kuma abin da bai shafeshi ba.
  7. Umarni da aikin alheri da hani na abin ƙi, da kuma nasiha daga abin da ya shafi mutum; domin cewa shi abin umarta ne da su.
  8. Yana shiga cikin gamewar ma'anar hadisin: Nisanta daga abin da bai shafi mutum ba na abin da Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya haramta da kuma abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya ƙi shi, haka nan abin da ba'a buƙatuwa zuwa gareshi na al'amuran lahira, kamar haƙiƙanin gaibu da rarrabe-rarraben hukunci a cikin halitta da umarni, daga cikinsu akwai tambaya da bincike game da mas'alolin da aka ƙaddara da waɗanda ake sa ran zasu faru waɗanda ba su faru ba, koma basu kusa su faru ba, koma ba'a suranta faruwarsu ba.
Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci الأمهرية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الدرية الصربية الطاجيكية Kinyarwanda المجرية التشيكية الموري Kanadische Übersetzung الولوف Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية الجورجية المقدونية الخميرية
Manufofin Fassarorin