عَنْ عَلِيٍّ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ
كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُقْرِئُنَا القُرْآنَ عَلَى كُلِّ حَالٍ مَا لَمْ يَكُنْ جُنُبًا.
[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي وابن ماجه وأحمد] - [سنن الترمذي: 146]
المزيــد ...
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana karantar da mu Alƙur'ani a kowanne hali muddin dai bai kasance yana da janaba ba.
[Hasan ne] - - [سنن الترمذي - 146]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koyar da sahabbansa Alƙur'ani yana karantar da su shi a dukkanin halayensa muddin dai bai kasance yana da janaba ta hanyar jima'i ba.