عن عائشة رضي الله عنها قالت:
كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَذْكُرُ اللهَ عَلَى كُلِّ أَحْيَانِهِ.

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 373]
المزيــد ...

Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ambaton Allah a kodayaushe.

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [Sahih Muslim - 373]

Bayani

Nana A'isha uwar Muminai Allah Ya yarda da ita, tana ba da bayanin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana tsananin kwaɗayi a kan yin ambaton Allah maɗaukaki, kuma ya kasance yana ambaton Allah a kowanne lokaci da kowanne yanayi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Ba a sharɗanta tsarkin ƙaramin hadasi ko babba a ambaton Allah ba.
  2. Dawwamar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ambaton Allah maɗaukaki.
  3. Kwaɗaitarwa a kan yawaita ambaton Allah maɗaukaki a kowanne lokaci domin koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai a yanayin da aka hana ambaton Allah kamar lokacin biyan buƙata.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (62)