عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رَضيَ اللهُ عنهُ:
أَنَّ رَجُلًا سَمِعَ رَجُلًا يَقْرَأُ: {قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ} يُرَدِّدُهَا، فَلَمَّا أَصْبَحَ جَاءَ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَذَكَرَ ذَلِكَ لَهُ، وَكَأَنَّ الرَّجُلَ يَتَقَالُّهَا، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ إِنَّهَا لَتَعْدِلُ ثُلُثَ القُرْآنِ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 5013]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'id al-Kudri - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa wani mutum ya ji wani mutum yana karanta: {Ka ce Shi ne Allah Shi kaɗai}, yana maimaita ta, lokacin da ya wayi gari sai ya zo wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya fada masa hakan, kai ka ce mutumin yana ganin ƙanƙantarta, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5013]
Abu Sa'id al-Khudr - Allah Ya yarda da shi - ya fadi cewa wani mutum ya ji wani mutumin daban yana karanta Suratu (Ikhlas): {Ka ce Shi ne Allah Shi kaɗai} yana maimaitata a kowanne dare ba ya ƙari akanta, lokacin da ya wayi gari sai ya zo gurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ambata masa haka, kamar shi mai maganar yana ganin cewa ta yi kaɗan, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa akan ma'anar ƙarfafawa: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai cewa ita (Surar) ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani.