عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ:
لَمَّا نَزَلَتْ عَلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ {لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ وَإِنْ تُبْدُوا مَا فِي أَنْفُسِكُمْ أَوْ تُخْفُوهُ يُحَاسِبْكُمْ بِهِ اللهُ فَيَغْفِرُ لِمَنْ يَشَاءُ وَيُعَذِّبُ مَنْ يَشَاءُ وَاللهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ} [البقرة: 284]، قَالَ: فَاشْتَدَّ ذَلِكَ عَلَى أَصْحَابِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَتَوْا رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ثُمَّ بَرَكُوا عَلَى الرُّكَبِ، فَقَالُوا: أَيْ رَسُولَ اللهِ، كُلِّفْنَا مِنَ الأَعْمَالِ مَا نُطِيقُ، الصَّلَاةَ وَالصِّيَامَ وَالجِهَادَ وَالصَّدَقَةَ، وَقَدِ اُنْزِلَتْ عَلَيْكَ هَذِهِ الآيَةُ وَلَا نُطِيقُهَا، قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَتُرِيدُونَ أَنْ تَقُولُوا كَمَا قَالَ أَهْلُ الكِتَابَيْنِ مِنْ قَبْلِكُمْ سَمِعْنَا وَعَصَيْنَا؟ بَلْ قُولُوا: سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ المَصِيرُ»، قَالُوا: سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ المَصِيرُ، فَلَمَّا اقْتَرَأَهَا القَوْمُ، ذَلَّتْ بِهَا أَلْسِنَتُهُمْ، فَأَنْزَلَ اللهُ فِي إِثْرِهَا: {آمَنَ الرَّسُولُ بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْهِ مِنْ رَبِّهِ وَالمُؤْمِنُونَ كُلٌّ آمَنَ بِاللهِ وَمَلَائِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لَا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِنْ رُسُلِهِ وَقَالُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ المَصِيرُ} [البقرة: 285]، فَلَمَّا فَعَلُوا ذَلِكَ نَسَخَهَا اللهُ تَعَالَى، فَأَنْزَلَ اللهُ عَزَّ وَجَلَّ: {لَا يُكَلِّفُ اللهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا اكْتَسَبَتْ رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذْنَا إِنْ نَسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا} [البقرة: 286] " قَالَ: «نَعَمْ» {رَبَّنَا وَلَا تَحْمِلْ عَلَيْنَا إِصْرًا كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِنَا} [البقرة: 286] قَالَ: «نَعَمْ» {رَبَّنَا وَلَا تُحَمِّلْنَا مَا لَا طَاقَةَ لَنَا بِهِ} [البقرة: 286] قَالَ: «نَعَمْ» {وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا أَنْتَ مَوْلَانَا فَانْصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الكَافِرِينَ} [البقرة: 286] قَالَ: «نَعَمْ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 125]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Lokacin da (ayar): {Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allah ne, idan kun bayyanar da abin da ke cikin ranku ko kuka ɓoyeshi Allah zai yi muku hisabi da shi, Yana gafartawa wanda Ya so kuma Yana azabtar da wanda Ya so, Allah Mai iko ne akan dukkan komai}.
[al-Baƙara: 284] ta sauka, ya ce: Sai hakan ya tsananta ga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - , sai suka zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sannan suka durƙusa akan gwiwowinsu, sai suka ce: Ya Manzon Allah, an ɗora mana ayyukan da zamu iya, sallah da azimi da jihadi da sadaka, haƙiƙa an saukar maka wannan ayar kuma ba zamu iyata ba, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Shin kuna son ku faɗi kamar yadda mazowa littafi biyu a gabaninku suka faɗa, mun ji mun saɓa?a'a ku ce: Mun ji mun bi, muna neman gafarKa ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa», suka ce: Mun ji kuma mun bi ya Ubangijinmu gafararKa muke nema makoma tana wurinKa, lokacin da mutane suka karantata, sai harsunansu suka horu da ita, a bayanta sai Allah Ya saukar da {Manzo ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa haka ma muminai, kowannensu ya yi imani da Allah da mala'ikunSa da littattafanSa da ManzanninSa bama banbanta wani daga cikin ManzanninSa, suka ce: Mun ji mun bi ya Ubangijinmu gafararKa muke nema makoma tana wurinKa}.
[al-Baƙara: 285], lokacin da suka aikata hakan sai Allah Ya shafe ta, sai ya saukar da {Allah ba Ya ɗorawa wata rai sai abin da zata iya, abin da ta aikata nata ne, haka abin da ta aikata na laifi yana kanta, ya Ubangijinmu kada Ka kamamu idan muka yi kuskure ko muka manta} [al-Baƙara: 286], ya ce: «Eh» {Ya Ubangijnmu kada Ka ɗora mana wani nauyi kamar yadda ka ɗorawa waɗanda ke gabanmu} [al-Baƙara: 286], ya ce: «Eh», {Ya Ubangijinmu kada ka ɗora mana abin da bazamu iya ba} [al-Baƙara: 286], ya ce: «Eh», {Ka yi mana rangwami Ka gafarta mana Kajiƙanmu Ka taimakemu akan mutane kafirai} [al-Baƙara: 286].
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 125]
Lokacin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukarwa AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -: {Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allah ne} halitta da mulki, da tasarrufi da jujjuya al'aura, {idan kuka bayyanar} kuka bayyanar kuka nuna {abin da ke cikin rayukanku} da ƙirazanku {ko kuka ɓoye shi} sai kuka ɓoyeshi a cikin zukatanku {Allah zai yi muku hisabinsa} a ranar alƙiyama. {Yana yin gafara ga wanda Yake so} da falalarSa da kuma rahamarSa, {Kuma Yana azabtar da wanda Yake so} da adalcinSa, {Allah Mai iko ne akan dukkan komai} wani abu ba ya gajiyar da Shi. Lokacin da sahabbai suka ji ta sai hakan ya yi musu tsanani; domin a cikinta akwai kama mutum har da abin da ke cikin zuciya na tinanika. Sai suka zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai suka durƙusa akan gwiwowinsu, sai suka ce: Ya Manzon Allah, kafin haka an ɗora mana ayyuka na jiki da zamu iya zuwa da shi; misalin sallah da azimi da jihadi da sadaka, sai dai haƙiƙa an saukar maka wannan ayar kuma mu ba zamu iyata ba. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce da su: Shin zaku faɗi irin abin da Yahudawa da Nasara suka faɗa: {Mun ji mun saɓa}? Kawai ku ce: {Mun ji mun bi gafararKa muke nema ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa}, sai sahabbai suka amsawa umarnin Allah da ManzonSa, sai suka ce; Mun ji mun bi gafrarKa muke nema ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa. Yayin da musulmai suka faɗeta da harsunansu, kuma rayukansu suka miƙa wuya gareta; sai Allah Ya saukar da tsarkakewa ga Annabi da kuma al'ummarsa da faɗinSa; {Manzo ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa muminai ma haka} harsunansu da zukatansu suka miƙa wuya gareta. {Kowannen su ya yi imani da Allah da mala'ikunSa da litattafanSa, da ManzanninSa, bamu banbancewa tsakanin wani daga cikin ManzanniSa}. Kai muna imani da su baki ɗaya {Suka ce Mun ji } faɗinKa {kuma mun bi} umarninKa, muna neman {gafararKa ya Ubangijinmu} da rangwaminKa, {makoma tana wurinKa} da makoma ranar da hisabi zai tsaya, yayin da suka aikata haka, kuma suka faɗi abin da aka umarce su da faɗinsa na bayyanar da ji da kuma bi ga umarnin Allah; sai Allah Yayi sauƙi ga wannan al'ummar Ya shafe waccar ayar da faɗinSa: {Allah ba Ya ɗorawa wata rai sai abin da zata iya} da ikonta da kuma ƙoƙarinta, {tana da} ladan {abin da ta aikata} na alheri, {kuma a kanta akwai} uƙubar {abin da ta aikata} na zunubi da laifi, kuma Allah ba Ya kama wani da laifin waninSa, haka da abin da zuciyarsa ta yi wasuwasi da shi. {Ya Ubangijinmu kada Ka kamamu} ka yi mana uƙuba {idan muka manta} bamu tuna ba, {Ko muka yi kuskure} sai muka bar daidai bada gangan ba, sai Allah Ya amsa musu hakan sai Ya ce: Haƙiƙa na aikata. {Ya Ubangijinmu kada Ka ɗora mana wani nauyi} da wahala da nauyi {Kamar yadda Ka ɗorawa waɗanda ke gabanmu} daga Banu Isra'il da wasunsu, sai Allah Ya amsa kuma Ya ce: Eh, haƙiƙa na aikata. {Ya Ubangijinmu kada Ka ɗora mana abin da bamu da ikon yin sa} na abubuwan taklifi da bala'i da al'amuran da muke gajiyawa daga ɗaukarsu, Allah Ya ce: Eh haƙiƙa na aikata, {Ka yi mana afuwar} zunubanmu Ka shafe mana su, {Ka gafarta mana} zunubanmu Ka suturta mana su, Ka yafe mana su, {Ka yi mana rahama} da rahamarKa yalwatacciya, {Kaine Majiɓincin al'amuranmu} kuma shugabanmu; {To Ka taimake mu} ta hanyar tsaida hujja da rinjaye {Akan mutane kafirai} a yaƙarsu, sai Allah Ya yi musu, sai Ya ce: Eh, haƙiƙa na aikata.