+ -

عَنْ عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ:
أَنَّ رَجُلًا مِنَ اليَهُودِ قَالَ لَهُ: يَا أَمِيرَ المُؤْمِنِينَ، آيَةٌ فِي كِتَابِكُمْ تَقْرَؤُونَهَا، لَوْ عَلَيْنَا مَعْشَرَ اليَهُودِ نَزَلَتْ لاَتَّخَذْنَا ذَلِكَ اليَوْمَ عِيدًا، قَالَ: أَيُّ آيَةٍ؟ قَالَ: {اليَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإِسْلاَمَ دِينًا} [المائدة: 3] قَالَ عُمَرُ: قَدْ عَرَفْنَا ذَلِكَ اليَوْمَ، وَالمَكَانَ الَّذِي نَزَلَتْ فِيهِ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَهُوَ قَائِمٌ بِعَرَفَةَ يَوْمَ جُمُعَةٍ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 45]
المزيــد ...

Daga Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa wani mutum daga cikin Yahudawa ya ce masa: Yakai sarkin muminai, Wata aya a cikin littafinku kuna karantata, da a ce agurinmu mu Yahudawa ta sauka da mun riƙi ranar idi, ya ce: Wacce aya ce? ya ce: {A yau ne na cika muku Addininku kuma na cika muku ni'imata kuma na yardar muku da Musulunci a matsayin Addini} [al-Ma'ida: 3] Umar ya ce: Haƙiƙa mun san wannan ranar, da gurin da ta sauka ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa alhali shi yana tsaye a Arfa a ranar Juma'a.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 45]

Bayani

Wani mutum daga cikin Yahudawa ya zo gurin sarkin muminai Umar - Allah Ya yarda da shi - kuma ya ce masa: Wata aya ce da kuke karantata a cikin littafinku Alƙur'ani, da ace mu jama'ar Yahudawa ne ta sauka a garemu a cikin littafinmu Attaura da mun maida wannar ranar idin da zamu dinga taruwa da shi; dan godiya ga ni'imar saukar wannan ayar mai girma, sai Umar - Allah Ya yardada shi - yace masa: Wace aya ce? Ya ce: {Kuma yaune Na cika muku Addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin Addini} Sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Haƙiƙa mun san wannan ranar, da gurin da ayar mai girma ta sauka a cikinsa, haƙiƙa ta saukane ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -a ranar idi, ita ce ranar Juma'a alhali shi yana tsaye a Arfa, kuma su ranaku biyu ne masu girma a wurin musulmai.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin abin da Umar - Allah Ya yarda da shi - yake a kansa na kulawa da wurin da ayar ta sauka da kuma lokacinta.
  2. Wannan ayar a cikinta akwai bayanin abin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi baiwa da shi ga wannan al'ummar, inda Ya cika mata Addininta, kuma Ya cika mata ni'imominSa, yadda bata buƙatar wani ƙari a cikin al'amarin Addini, duk abin da ya faru bayan Allah - Maɗaukakin sarki - Ya cika shi, in da ba shi da wani dalili daga gare shi da ake la'akari da shi (a matsayin) bidi'a ɓatacciya, kamar yadda hakan ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ya farar (da wani abu) a cikin al'amarinmu wannan abin da ba ya daga cikinsa, to shi abin juyarwa ne".
  3. Wannan hadisin za'a iya fahima daga gare shi cewa bukukuwan Idi basa kasancewa da ra'ayi da kuma ƙirƙira kamar yadda wasu daga cikin mazowa Littafi (Yahudawa da Nasara) daga gabaninmu suke aikata shi; kawai yana kasancewa ne da shari'a da kuma bi, to wannan ayar yayin da ta ƙunshi cika Addini da cika ni'imar da Allah Ya saukar da ita a cikin ranar da ya shara'antata idi ga wannan al'ummar ta fuska biyu:
  4. Na farkonsu: Cewa ita ce ranar idin mako ita ce ranar Juma'a.
  5. Na biyu: Ita ce ranar idin babbaban taro , ita ce lokacin taruwarsu mafi girma kuma wurin tsayuwarsu mafi girma (wato Arafat, ga Musulmai).
  6. Al-Sa'adi ya faɗa a cikin tafsirin wannan ayar: {Ayau ne Na cika muku Addininku} ta hanyar cikar nasara, da cika shari'u na zahiri da baɗini, tushe da kuma rassa, saboda haka ne Littafi da sunnah suka kasance sun isa dukkanin isa a cikin hukunce-hukuncen Addini tushensa da kuma rassansa, duk mai ɗorawa kansa aiki wanda yake riya cewa babu makawa ga mutane a cikin sanin aƙidunsu da kuma hukunce-hukuncensu zuwa wasu ilimai waɗanda ba ilimin Littafi da sunnah ba, daga ilmul kalam da waninsa, to shi jahili ne, mai ɓarna a cikin da'awarsa, ya riya cewa Addini baya cika sai da abin da ya faɗeshi kuma yayi kira zuwa gareshi, wannan yana daga cikin mafi girman zalinci da dangantawa Allah da ManzonSa jahilci, {Kuma Na cika muku ni'imata} ta zahiri da baɗini {Kuma na yardar muku da Musulunci a matsayin Addini} wato: Na zaɓar muku shi a matsayin Addini, kamar yanda na yardar muku da shi, sai ku tsaya a kansa dan godiya ga Ubangijinku, ku gode maSa abin da Yayi muku baiwa da mafificin Addinai kuma mafi ɗaukakarsu kuma mafi cikarsu.
Fassara: Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Vietnam Kurdawa Portuguese Yaran Tailand Asami الهولندية الدرية المجرية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin