عَنْ سَلْمَانَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
قَالَ لَنَا الْمُشْرِكُونَ: إِنِّي أَرَى صَاحِبَكُمْ يُعَلِّمُكُمْ حَتَّى يُعَلِّمَكُمُ الْخِرَاءَةَ، فَقَالَ: أَجَلْ، إِنَّهُ نَهَانَا أَنْ يَسْتَنْجِيَ أَحَدُنَا بِيَمِينِهِ، أَوْ يَسْتَقْبِلَ الْقِبْلَةَ، وَنَهَى عَنِ الرَّوْثِ وَالْعِظَامِ وَقَالَ: «لَا يَسْتَنْجِي أَحَدُكُمْ بِدُونِ ثَلَاثَةِ أَحْجَارٍ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 262]
المزيــد ...
Daga Salman - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Mushirikai suka ce mana: Lallai cewa ni ina ganin abokin nan naku yana koya muku (abubuwa) har yana koya muku biyan buƙata, sai ya ce: Eh, Lallai cewa shi ya hana ɗayanmu ya yi tsarki da (hannun) damansa, ko ya fuskanci alƙibla, kuma ya yi hani daga (tsarki) da toroson dabbobi ko ƙasusuwa kuma ya ce: «Kada ɗayanku ya yi tsarki da ƙasa da duwatsu uku».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 262]
Salman al-Fasrsi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mushrikai suka ce mana, suna masu izgili: Lallai Annabinku yana koya muku kowane abu, har yana koya muku ta yaya zaku biya buƙatarku ta fitsari ko bahaya! Salman ya ce: Eh, ya sanar da mu ladubban biyan buƙata; daga cikin hakan cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hanamu mu yi tsarki da hannun dama bayan biyan buƙata dan kiyaye shi daga najasa da kuma girmamawa, ko mu fuskanci Ka'aba a lokacin yin fitsari ko bahaya, kuma ya yi hani daga yin tsarkin hoge da toroson dabbobi da kuma ƙasusuwansu, kuma wanda ya yi kari (hadasi) kada ya wadatu a tsarkin hoge da ƙasa da duwatsu uku.