عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ إِذَا خَرَجَ مِنَ الغَائِطِ قَالَ: «غُفْرَانَكَ».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 30]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita -:
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya fito daga bayan gida yana cewa: "Ina neman gafararKa".
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 30]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya fito daga biyan buƙatarsa na bayan gida yana cewa: Ina roƙonKa (gafararKa) ya Allah.