عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
إِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَهَى أَنْ يُسْتَنْجَى بِرَوْثٍ أَوْ عَظْمٍ، وَقَالَ: «إِنَّهُمَا لَا تُطَهِّرَانِ».
[صحيح] - [رواه الدارقطني] - [سنن الدارقطني: 152]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga yin tsarki da toroson dabbobi ko ƙashi, kuma ya ce: «Lallai su basa tsarkakewa».
[Ingantacce ne] - [Al-Dar Al-Kutni Ya Rawaito shi] - [سنن الدارقطني - 152]
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya biya buƙatarsa na fitsari ne ko bahaya ya yi tsarkin hoge da ƙashin dabbobi ko torosonsa da busassun torosonsa; kuma ya ce: Lallai su basa kawar da najasa, kuma ba'a tsarkaka daga garesu.