عَنْ أَبِي أُمَامَةَ البَاهِلِيِّ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: ذُكِرَ لِرَسُولِ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلاَنِ أَحَدُهُمَا عَابِدٌ وَالآخَرُ عَالِمٌ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«فَضْلُ العَالِمِ عَلَى العَابِدِ كَفَضْلِي عَلَى أَدْنَاكُمْ»، ثُمَّ قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ اللَّهَ وَمَلاَئِكَتَهُ وَأَهْلَ السَّمَوَاتِ وَالأَرَضِينَ حَتَّى النَّمْلَةَ فِي جُحْرِهَا وَحَتَّى الحُوتَ لَيُصَلُّونَ عَلَى مُعَلِّمِ النَّاسِ الخَيْرَ».
المزيد
Daga Abu Umama al-Bahili - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An ambatawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane biyu ɗayansu mai ibada ne ɗayan kuma malami ne, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
«Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan wanda ke ƙasanku», sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai Allah da mala'ikunSa da waɗanda ke sammai da ƙassai har tururuwa a cikin raminta kai har kifi suna addu'a ta alheri ga wanda yake koyar da mutane alheri».